AUNA FAHIMTA Karanta wadannan labarai, sannan ka amsa tambayoyin da ke biye. Idan mutum ya kama sana’a, musamman a cikin sana’ o’ in Hausa na…

JAMB Hausa 2024 215 views
Source: JAMB · 2024

AUNA FAHIMTA

Karanta wadannan labarai, sannan ka amsa tambayoyin da ke biye.

Idan mutum ya kama sana’a, musamman a cikin sana’ o’ in Hausa na gargajiya tamkar ya shiga wani kulob ne. Dalili kuwa, kowace sana’ar Hausa ta gargajiya za ka iske tana da wadansu al’adu nata daban. Misali an san Mahauta a kan al’adar hawan kaho, da kuma iya mayar da magana. Sa’annan an san Makera da wasan cin-wuta, su ko Maharba kan bayar da magunguna irin na saiwa da sassake-sassake, da sauransu. Wasu sana’o in har unguwanni gare su a cikin birane. Saboda haka idan bakon mai sana’a ya shigo gari, yakan nemi unguwar masu sana’a irin tasa ne, ya je ya zauna. Zaman irin wannan unguwar zama ne na cude-ni-in-cude-ka wajen aiki, ko a fagen kayan aiki, ko wajen dabarun samun kasuwa, da sauransu. Sa’annan dukkan sana’o’ i suna da sorakuna, masu kula da zamansu a gari. Kuma su ne tsani daga masu sana’a zuwa ga hukumar gari ko kasa. Misali akwai Sarkin gini, da Galadiman gini, da Madakin gini, da Wakilin gini, da Sarkin fawa, da Wakilin fawa, da Sarkin aska, da Dangaladima, da Sarkin Makera, da sauran irinsu. Al’adar ‘iya mayar da magana’ ta kebanta gaTamkar ya shiga wani kulob ne’. Kalmar da aka ja wa layi na nufin

  1. al’ada
  2. kungiya ✓
  3. sana’a
  4. sarauta
Explanation

The phrase “tamkar ya shiga wani kulob ne” compares joining an occupation to joining a club. The word “kulob” comes from the English word “club.”

In Hausa, a club or association is called “kungiya.” This is a group of people who share common interests. When you join an occupation, you become part of that group.

The passage uses this comparison to show that occupations have their own communities and rules. Just like a club has members who follow certain practices.

Was this explanation helpful?