AUNA FAHIMTA Karanta wadannan labarai, sannan ka amsa tambayoyin da ke biye. Idan mutum ya kama sana’a, musamman a cikin sana’ o’ in Hausa na…

JAMB Hausa 2024 209 views
Source: JAMB · 2024

AUNA FAHIMTA

Karanta wadannan labarai, sannan ka amsa tambayoyin da ke biye.

Idan mutum ya kama sana’a, musamman a cikin sana’ o’ in Hausa na gargajiya tamkar ya shiga wani kulob ne. Dalili kuwa, kowace sana’ar Hausa ta gargajiya za ka iske tana da wadansu al’adu nata daban. Misali an san Mahauta a kan al’adar hawan kaho, da kuma iya mayar da magana. Sa’annan an san Makera da wasan cin-wuta, su ko Maharba kan bayar da magunguna irin na saiwa da sassake-sassake, da sauransu. Wasu sana’o in har unguwanni gare su a cikin birane. Saboda haka idan bakon mai sana’a ya shigo gari, yakan nemi unguwar masu sana’a irin tasa ne, ya je ya zauna. Zaman irin wannan unguwar zama ne na cude-ni-in-cude-ka wajen aiki, ko a fagen kayan aiki, ko wajen dabarun samun kasuwa, da sauransu. Sa’annan dukkan sana’o’ i suna da sorakuna, masu kula da zamansu a gari. Kuma su ne tsani daga masu sana’a zuwa ga hukumar gari ko kasa. Misali akwai Sarkin gini, da Galadiman gini, da Madakin gini, da Wakilin gini, da Sarkin fawa, da Wakilin fawa, da Sarkin aska, da Dangaladima, da Sarkin Makera, da sauran irinsu. Al’adar ‘iya mayar da magana’ ta kebanta gaSana’o’ in Hausa na gargajiya sun kunshi wadannan al’adu in ban da

  1. bayar da magani
  2. hawan kaho
  3. sarauta
  4. zaman unguwa. ✓
Explanation

The passage lists several customs of traditional Hausa occupations. These include giving medicine, ceremonial activities, and leadership titles. These are all specific to certain occupations.

However, “zaman unguwa” (living in neighborhoods) is not a unique custom. It is a general practice where people with similar occupations live near each other. This applies to all occupations, not just one.

The question asks which is NOT a unique custom. Living in neighborhoods is common to all, so it is the correct choice.

Was this explanation helpful?