Karanta wadannan labarai, sannan ka amsa tambayoyin da ke biye da su. Hausawa sukan sami suna daga lokaci ko hali korana ko yanayi ko faruwar wani…
Karanta wadannan labarai, sannan ka amsa tambayoyin da ke biye da su. Hausawa sukan sami suna daga lokaci ko hali korana ko yanayi ko faruwar wani abu. Alalmisali,idan aka haifi yaro a wani lokaci kamar, dare sai akira shi ‘Dandare, in kuwa da hantsi ne sai akira shi Nahantsi ko Magawata idan an haife shi a farkon wata. ko Ciwake idan lokacin ana cin wake, ko Damina idan ana ruwan sama. Idan kuwa aka haifi yaro a wata rana sai a ba shi Suna da irin wannan ranar; kamar Danliti ko Attine,ko Tanimu ga wanda aka haifa ran Litinin, idan kuwa Talata ce akan kira yaro da suna Dantala.ko Taku ko Lantana ko Talatu. Haka kuma Laraba ko Larai. Alhamis kuwa Lami ko Danlami. Najuma ko Danjuma da Juma ko Jummai suneya’yan Juma’a. Dan Asabe ko Asabe ko Assibi ko Subdu su ne aka haifa ran Asabar. Akwai kuma sunayen da ake sa wa yaro dangane da halayyar da aka haife shi a ciki. Misali: Talle wanda uwarsa ta mutu lokacin haihuwa ko Audi wanda ubansa ya mutu yana ciki. Idan kuwa aka haifi namiji bayan ‘ya’ya mata uku ko fiye shi ne Mato, ko Delu ko Kande ko Dela ga wadda ta biyo maza da yawa. Gambo kuwa wanda aka haifa bayan tagwaye.
Yaron da aka haifa lokacin ruwan sama shi ne
Explanation
Damina is the name for a child born during rainfall. This name connects to the weather at birth time.
The other names relate to different events. Ciwake is for birth during a meal. Dandare is for night births. Magawata is for first day of the month.
Hausa naming traditions link a person to the time or event of their birth.