Damukowa mutum ne wanda irin halayensa ne suka sa ake kiransa da wannan suna. Domin yana da kinibibi, da gulma, da keta da rashin mutunci da rashin…

Damukowa mutum ne wanda irin halayensa ne suka sa ake kiransa da wannan suna. Domin yana da kinibibi, da gulma, da keta da rashin mutunci da rashin ganin kimar kowa. Kuma yana kiwon dabbobi kamar jakai da rakuma da rakuma da tumakai da kaji har da shanu. Asalin garin Damukowa shi ne Gunu wanda idan za a je garin sai an keta dazuzzuka da rafuka, kuma ana cin karo da dabbobbin daji kamar birai da kuraye da macizai da giwaye amma babu damisa da zaki. Idan damina ta sauka Mai unguwar Gunu kan umurci jama’a da su d’aure dabbobinsu don kar su yi barnar amfanin gonarsu kamar masara da dawa da gyada da wake amma ban da auduga domin ba sa noma ta. Nan ne fa Damukowa kan nuna halayensa na rashin ga umurnin Mai unguwa na kin daure dabbobinsa. Idan dabbobinsa sun yi barna a gonakin mutane yakan bijire wa dogaran da suka zo kama shi har ya sa a yi musu duka du keta musu tufafi, har ma da ji musu ciwo. Garin Gunu na makwabtaka da Shakwatu da Gwada da Badum da Akope. Cikin mutanen wadannan garuruwa akwai maharba da masunta da makiyaya da manoma amma babu madora.Wane abu ne mutanen garin Gunu ba su nomawa?

  1. Auduga ✓
  2. Dawa
  3. Gyada
  4. Masara

Explanation

Auduga is cotton. The passage clearly states people do not farm cotton in Gunu.

They grow masara (corn), dawa (guinea corn), gyada (groundnuts), and wake (beans). The chief orders animals tied up to protect these crops.

Cotton is mentioned as the exception to what they farm.